Masu iya Magana sun ce “Yawan Mutane shine Kasuwa ba tarin rumfuna ba”. Duk da cewa wannan Magana haka take kuma kowa ya tabbatar da hakan, sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci hakan ba a cikin harkar kasuwanci, musamman ma idan aka danganta wannan zancen da fasahar sadarwar zamani ta Internet. Mafi yawancin mutane har yanzu basu fahimci irin tasirin da amfani da kafofin sada zumunta irinsu Facebook, WhatsApp da Instagram zasu iya yi ba wajen ciyar da harkar kasuwancinsu a gaba. Wasu ma kawai su tunaninsu akan wannan kafa bai wuce na yin chatting ba da kuma karanta labaran ban nishadi.
A cikin wannan kasidar tamu ta wannan lokaci, mun yi sharhi na musamman akan yanda zaku iya amfani da Facebook, WhatsApp da kuma Instagram wajen tallata hajojinku ko kuma kasuwancinku cikin sauki kuma a kyauta.
Sanin kowa ne cewa babban abin da harkar kasuwanci ke bukata shine mutane su san da kai kuma su san da kasuwancinka. Wannan ne ya sanya a lokutan da suka gabata, masana’antu da kuma kamfanoni suke kokari a ko da yaushe ganin cewa sun sayi fili wanda za’a saka tallace-tallacensu a cikin Rediyo, TV, jarida da dai sauran kafofin yada labarai. Kasancewar irin wadannan tallace-tallace na TV ko kuma Rediyo kudi ake biya, ya sanya kanana da kuma matsakaitan ‘yan kasuwa kasa samun wannan damar. Wannan ne dalili ne ya sanya kananun masan’antu ke daya daga cikin wadanda suka fi kowa farin cikin da shigowar fasahar sadarwa ta internet, domin tana basu dama su isar da sakonsu zuwa ga mutane da dama ba tare da sun biya ko da sisin kobo ba.
Facebook, WhatsApp da kuma Instagram na daya daga cikin shafukan sada zamunta da suka fi ko wadanne yawan jama’a masu amfani da su. Wannan ne ya sanya muka zabe su wajen nuna muku yanda zaku iya amfani da kafafen sada zumunta wajen ciyar da harkar kasuwancinku a gaba. Ga bayanin yanda zaku iya yin hakan daya bayan daya:
Facebook shine kafar sadarwa da yafi yawan mutane a duniya. Akwai bangarorin Facebook da dama da zaku iya amfani da su wajen tallata harkar kasuwancinku ko kuma wani aiki da kuke yi. Wadannan bangarori sune kamar haka:
Group:- Group wani sashe ne na facebook da ke hada mutane masu irin akida ko kuma tunani iri daya. Zaku iya amfani da wannan dama domin tallata hajarku ko kuma wani aiki da kuke gudanarwa ga sauran mutanen wannan group, ta hanyar sharing na hotuna ko kuma rubutu. Za kuma ku iya kirkirar wani group naku na kanku da zaku iya sanya masa sunan kasuwancinku, ta yanda duk wanda ke da sha’awa zaya iya shiga a ciki.
Posing:- Wata hanya kuma da zaku iya tallata kayanku a saman facebook shine ta hanyar yin posting na hotuna ko kuma rubutu a kan wannan kasuwanci naku da kuke gabatarwa. A maimakon yin sharing na labarai da basu da wani tasiri a kanku, yin posting dangane da kasuwancinku zaya baku dama sauran abokananku da kuma wasu sauran mutane su iya ganin wannan post naku, a lokaci guda kuma, zasu iya jin bukatar siyen wannnan kaya naku.
Page:- Hanya ta ukku kuma da zaku iya amfani da iya wajen tallata kasuwancinku shine ta hanyar kirkirar page. Shima wannan page zaku iya sanya masa sunan kasuwancinku kamar dai yanda kuka yi a group, amma bambancin page da group shine, a group kowa zaya iya yin posting, amma a page mai page din ne kawai zaya iya yin rubutu kowa ya gani a ciki.
Chat:– Hanyar ta hudu kuma da zaku iya amfani da facebook wajen tallata kasuwancinku ita ta hanyar yi ma abokananku talla kai tsaye ta hanyar tura masu sakon talla. Wannan zaya basu damar yi maku tambaya kai tsaye akan wannan kasuwanci naku, kamar farashin yanda kuke siyar da kayan. Yi ma mutum talla kai tsaye ta hanyar message zaya sanya yaji cewa kun damu da shi, shima yayi kokarin ganin cewa ya mayar da biki wajen siyen wadannan kaya naku.
Baya ga Facebook, WhatsApp shine kafar sada zumunta mafi daukar yawan jama’a. Zamu iya cewa damar da WhatsApp ke bayarwa ta tallata kasuwanci ta fi wacce facebooke ke bayarwa, domin kuwa, a WhatsApp kai tsayen kuna mu’amala ne da mutumin da kuke yi ma talla. Duk da cewa wasu mutane na amfani da group wajen tallata kayansu a WhatsApp, ba kowa ne ya fahimci cewa Status da kuma Broadcast list sun fi amfani wajen yi ma mutane talla.
Status: Sanin kowa a yanzu akwai mutane da yawa da ba zasu taba hawan WhatsApp ba, ba tare da sun duba Status update da sauran abokansu ba. To tunda haka ne, wannan kuwa babbar dama ce da zaku iya amfani da ita wajen dora hotuna na kasuwancin da kuke yi ta yanda duk wanda ya duba zaya iya gani, a lokaci guda kuma ya iya yin tayi akan wannan abu naku.
Broadcast List:- Shi broadcast list wani list zaku iya hadawa na mutanen da kuke da lambobinsu, ta yanda a duk lokacin da kuka bukaci tura ma wadannan mutane sakonninku, kai tsaye zaku shiga cikin wannan list din ne sai ku tura sakon, a lokaci guda kuma zaya kai ga duk wanda ke cikin wannan list din. Abun da ya bambanta Broadcast list da kuma Group shine, a group kowa zaya iya yin Magana, a yayin da kuma a broadcast list, mai list din ne kawai zaya iya cewa wani abu.
Zaya yi wuya a wannan lokaci ka ga matashin da bai san cewa ana amfani da Instagram domin rarraba sakunan hoto da kuma na video. Tunda haka ne, a kunga ke nan zaku iya amfani da wannan babbar dama wajen isar da sakon kasuwancinku ga sauran mutane ta hanyar sanya hoto ko kuma video mai dauke da wannan sako naku.
Wadnnan sune hanyoyi da zaku iya bi domin tallata kasuwanci a saukake ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta, ba tare da kun biya ko da sisin kobo ba.